Sakamakon nuna yarda da gamsuwa da jagorancin Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, Kimanin kungiyoyin jihar Zamfara 102 suka yi karo-karo suka tara naira miliyan 50 domin saya masa fom din takarar gwamna Karo na biyu a 2023
Saboda haka ne jam'iyar Apc ta jihar Zamfara ke gayyatar dukkanin halatattun yayan jam'iyar Apc na jihar zuwa wajen gangamin gabatar da cak din ga mai daraja Gwamnan jihar Zamfara Hon Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun karkashin jagorancin Shugaban jam'iyar Apc na jihar Zamfara Hon. Tukur Umar Danfulani
Za a hadu a Babban Masallacin idi da ke Tudun Wada Gusau da karfe 8:00 na safe ranar Jumu'a 6/5/2022 inda za a taka zuwa Fadar gwamnatin jihar domin mika cak din ga Gwamnan
Shugaban jam'iyar na kara nuna godiyarsa ga Allah da al'ummar jihar Zamfara akan irin Soyayya da su ke nunawa gwamnatinsu tare da rokonsu da su cigaba da baiwa gwamnatin goyon baya.
Haka zalika Shugaban ya nuna matukar godiyarsa ga wadannan kungiyoyin da sauran magoya bayan wannan gwamnatin tare da tabbatar da masu da cewa jam'iyar Apc ba za ta taba yar da su ba
Yusuf Idris Gusau
Sakataren yada labarai na jam'iyar Apc na jihar Zamfara
5th May, 2022
0 Comments